17 Satumba 2025 - 11:06
Source: ABNA24
Tawagar Sojojin Isra'ila Ta Ziyarci Birnin Alkahira Domin Ci Gaba Da Gudanar Da Ayyukan Tsaro Da Masar

Jaridar Al-Zaman, ta nakalto majiyar ta cewa, wata tawagar sojojin Isra'ila ta ziyarci birnin Alkahira domin ci gaba da gudanar da harkokin tsaro da kasar Masar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Jaridar ta kara da cewa: Ziyarar tawagar sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a birnin Alkahira ta gudana ne a yayin da shugabannin kungiyar Fatah suka bukaci kungiyar Hamas da ta mika fayil din fursunonin da tattaunawa da suke da Isra'ila ga shugabancin kasar Masar, domin kuwa wannan kasa ita ce a daya tilo da ke da griman ikon kasa da kasa da na shiyya-shiyya don matsawa Isra'ila lamba domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma janyewar Tel Aviv daga zirin Gaza.

A cewar Al-Zaman, masu fafutukar siyasa sun gudanar da zanga-zanga a gaban kungiyar 'yan jarida ta Masar, kuma bisa la'akari da yakin da Isra'ila ke ci gaba da yi da Falasdinawa a zirin Gaza, sun yi kira ga shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da ya kawo karshen yarjejeniyar Camp David da Tel Aviv da kuma daina daidaita alaka da Isra'ila.

Your Comment

You are replying to: .
captcha